Shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Masri Al-Youm ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke kula da masallacin harami da masallacin Annabi (SAW) ta sauya kyallen dakin Ka’aba a yammacin ranar Talatar da ta gabata 18 ga watan Yuli, kamar yadda ake gudanar da ibada a kowace shekara da kuma jajibiri na sabuwar shekarar musulunci.
Wannan labule da aka shirya a Majalisar Sarki Abdulaziz don yin saƙar labulen Ka'aba, za a maye gurbinsa da labulen da ya gabata ta hanyar halartar masana da kuma wata ƙungiya ta musamman da aka horar da su don wannan aikin.
Tawagar ta musamman ta fara da sauke tsohon labule mataki bayan mataki sannan ta sanya sabon labulen Ka'aba.