IQNA

16:03 - December 19, 2023
Lambar Labari: 3490333

Daren karshe na zaman makokin Sayyida Zahra (AS) tare da halartar jagora

Tehran (IQNA) A daren jiya ne aka gudanar da zaman makokin Sayyida Fatima Zahra (AS) a Husainiyar Imam Khumaini (RA) tare da halartar jagoran juyin juya halin Musulunci.

Daren karshe na zaman makokin Sayyida Zahra (AS) tare da halartar jagora

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman makokin Sayyida Fatima Zahra (a.s) na karshe a daren jiya tare da halartar Jagoran juyin juya halin Musulunci da wasu gungun jama'a a Husainiyar Imam Khumaini. (RA).

Hojjatul Islam da Al-Muslimin Abedini, a cikin jawabin da suka yi dangane da tarihin Sayyida Zahra (a.s), sun yi bayani kan wajibci da bukatuwar zamani na sanin koyarwar gidan Fatima don fadakar da al’umma.

A cikin zaman makoki, Saeed Haddadian da Mohammad Hossein Haddadian suma sun gabatar da yabo ga Siddiqa Kobari (AS).

 

4188673

 

captcha