IQNA

18:26 - December 30, 2023
Lambar Labari: 3490389

Bishiyar Kirsimeti a Karbala da soke bukukuwan a Kirkuk

Karbala (IQNA) Gwamnan Karbala ya sanar da cewa, za a dauki mataki mai tsanani ga mutanen da suke da niyyar cin mutuncin birnin da kuma sunan addini na Karbala, sannan ya ba da umarnin tattara bishiyar Kirsimeti a fadin lardin daga jiya Juma'a.

Bishiyar Kirsimeti a Karbala da soke bukukuwan a Kirkuk

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Barratha cewa, shugaban kwamitin kolin tsaro kuma gwamnan Karbala Nasif al-Khattabi ya jaddada cewa, za a dauki tsauraran matakai don tunkarar mutanen da suke da niyyar cin mutuncin birnin Karbala. An cire itatuwan kirsemiti da aka gani a titunan birnin na Karbala a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan sabuwar shekara tare da kawar da wadannan bishiyun daga titunan birnin na Karbala.

 

 

 

4190712

 

captcha