IQNA

Bayani da harshen Ibrananci na shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci game da laifin kisan kiyashi na gwamnatin mamaya

21:22 - January 12, 2024
Lambar Labari: 3490461
Tehran (IQNA) Shafin twitter na ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatullah Khamenei ya wallafa wata jimla na Jagoran juyin juya halin Musulunci a harshen yahudanci a daren Laraba 10 ga watan Janairu.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Khamenei.ir na X (Twitter) ya fitar da wasu sabbin jimloli na jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Ibraniyanci a ranar Laraba.

A cikin rubutun wannan sakon an bayyana cewa: Ba za a manta da laifuffukan da gwamnatin Sahayoniya ta aikata ba, har ma bayan an ruguza wannan gwamnati da kuma shafe ta daga doron kasa, wadannan laifuffuka da kashe dubban yara da mata. za a rubuta a cikin littafai."

 

4193330

 

captcha