Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Yum Sabe cewa, hoton kyakkyawan karatun wani matashi dan kasar Masar mai suna Mahmoud Adel Abdel Sami tare da abokinsa daga ayoyin suratu Taha ya dauki hankulan masu amfani da shafukan sada zumunta. A cikin wannan bidiyon, ya karanta wadannan ayoyi daga cikin suratu Taha.