Taron ya kuma kasance wani lokaci na tunawa da marigayi shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, inda 'yan takara da dimbin mahalarta taron suka nuna girmamawa.
Taron dai ya gudana ne a daidai lokacin da kasar Iran ke juyayin mutuwar shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da tawagar da suke tare da su a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar ranar Lahadi. Iran na gudanar da zaman makoki na kwanaki biyar, inda a yau ne za a fara gudanar da jana'izar.
An kuma shirya taruka na musamman a zagayen karshe na gasar da aka shafe sa’o’i biyar ana yi domin tunawa da irin hasarar rayuka da aka yi.