A cewar al-Mayadeen, mahaifiyar Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta rasu.
Tashar Al-Manar ta bayar da rahoton cewa: "Mahdia Safiuddin" da aka fi sani da "Umm Hassan" kuma matar Abdulkarim Nasrallah ta rasu bayan ta yi fama da jinya.
Za a yi jana'izar ne a ranar Lahadi 6 ga watan Yuni a makabartar Roudah al-Shahidin.