IQNA

An yi Sallar mamaci ga’ib ga shahidan hidima a Tanzaniya

15:29 - May 26, 2024
Lambar Labari: 3491223
IQNA - Babban Mufti na kasar Tanzaniya, a yayin shahadar shahidan hidima, ya gabatar da addu'a  ga wadannan shahidan.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa,  Sheikh Abu Bakr bin Zubair bin Ali babban mufti na kasar Tanzaniya ya bayyana cewa, shahadar Ayatullah Ibrahim Raisi, shahidi Amir Abdullahian da sauran shahidai, labari mai cike da tashin hankali da sanya bakin ciki, sannan a sa'i daya kuma, ya isar da sakon ta'aziyyar wannan lamari a madadinsa da na musulmin kasar Tanzaniya, ya mika ta'aziyyarsa ga jakadan Iran a Tanzaniya, da shugabanni da al'ummar Iran.

Ya kuma halarci ofishin jakadancin kasar Iran domin jajantawa tare da sanya hannu kan littafin tunawa da shahidan.

Har ila yau babban Mufti na kasar Tanzaniya ya gudanar da sallar jana'izar a babban masallacin sa kwana guda bayan binne gawar shahidan.

An gudanar da wannan addu'a ne a masallacin mufti tare da halartar ma'abota addini, da kuma wakilin ofishin jakadancin kasar Iran.

پیام تسلیت مفتی تانزانیا به مناسبت شهادت آیت الله رئیسی

پیام تسلیت مفتی تانزانیا به مناسبت شهادت آیت الله رئیسی

پیام تسلیت مفتی تانزانیا به مناسبت شهادت آیت الله رئیسی

 

4218301

 

 

 

 

captcha