IQNA

Musuluntar dan wasan tawagar kasar Uganda

15:51 - July 12, 2024
Lambar Labari: 3491499
IQNA - Travis Mutiba, dan wasan tawagar kasar Uganda kuma kwararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Zamalek ta Masar, ya bayyana Musulunta a ranar Talata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera Mubasher cewa, Travis Mutiba dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Uganda kuma kwararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Zamalek ta kasar Masar ya sanar da Musulunta a yau Talata.

'Yan wasan Zamalek sun bayyana cewa abokin wasansu Mutiba ya musulunta tare da taya shi murna bayan ya canza sunansa zuwa Jamal.

Dan wasan tsakiyar Zamalek Mohammad Ashraf ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa: Barka da zuwa Musulunci yayana Jamal. Shima dan wasan Tunisia Hamzeh Maslouthi ya taya Motiba murnar musulunta da kuma canza sunansa ta hanyar buga hoto da shi.

Motibah ya koma kungiyar Zamalek ta Masar a watan Janairun da ya gabata kuma yadda ya taka rawar gani ya ja hankalin mutane da yawa. Wannan dan wasan na kasar Uganda, a lokacin canja wuri na hunturu na karshe, ya rattaba hannu kan kwantiragin sayan sa na kaka 4 da rabi zuwa kungiyar Masar, Zamalek.

 

 

 
 

 

 

 

captcha