
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau juma’a 29 ga watan yuli masu juyayin Husaini sun gudanar da gagarumin taron a birnin Kigoma na kasar Tanzaniya, na ranar shahadar Aba Abdullah al-Hussein (a.s). da kuma garkuwa da Ahlul Baiti (a.s.).
A cikin wannan biki da ya samu halartar malamai da dalibai da sauran al'umma da masu tablig da daruruwan mabiya Husaini, an gabatar da jawabai inda masana suka yi tsokaci kan bala'in day a faru kan ahlul bait a wannan waki’a.






