IQNA

15:23 - July 24, 2024
Lambar Labari: 3491569

Mabiya mazhabar Shi’ar California sun yi zaman makokin shahadar Imam Husaini

IQNA - Wasu gungun mabiya mazhabar Shi'a daga birnin San Jose na jihar California sun gudanar da zaman makokin shahadar Aba Abdullah al-Hussein (a.s) da sahabbansa muminai tare da shirye-shirye na musamman na yara.

Mabiya mazhabar Shi’ar California sun yi zaman makokin shahadar Imam Husaini

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mabiya mazhabar shi’a da iyalan gidan manzon Allah (SAW) a birnin San Jose sun halarci cibiyar musulunci ta Saba a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyi na addinin muslunci na mabiya mazhabar shi’a a Amurka domin gudanar da tarukan tunawa da shahadar Imam Husaini (a.s).

Har ila yau, yara sun yi jimamin tuta na hubbaren Sayyid Al-Shohada (AS) a cikin Husseiniyyah mai albarka.

Saba Islamic Center daya daga cikin cibiyoyin Musulunci a San Jose, California, Amurka. An kafa wannan cibiya a shekarar 1979 kuma ta ci gaba da ayyukanta na addini da na al'adu har zuwa yanzu.

 

 
 

 

 

 

 

captcha