IQNA

Tutar Haramin Imam Ridha ta Canza yayin da aka kawo karshen Tattakin Makoki

IQNA – A wani biki da aka yi a ranar 7 ga Satumba, 2024, an maye gurbin bakar tutar da ke saman hubbaren Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad da wata kore. Canjin tuta dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman makoki a watannin Muharram da Safar da zuwan Rabi’ul Awwal.