Watan Ramadan shi ne wata na tara kuma daya daga cikin watanni mafi tsarki a kalandar Musulunci, wanda ya ke shiga tsakanin watannin Sha’aban da Shawwal. Wannan wata ya dauki matsayi na musamman a tsakanin musulmi, domin shi ne watan da aka ambaci sunansa karara a cikin Alkur'ani mai girma.
Aya ta 185 a cikin suratu Baqarah ta bayyana karara cewa an saukar da kur’ani mai girma ga Annabi Muhammad (SAW) a cikin wannan wata, kuma hakan ya sanya watan Ramadan ya zama wata fitattu da albarka.
Kalmar “Ramadan” a zahiri tana nufin tsananin zafin rana, kuma an ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa ana kiran wannan wata Ramadan ne domin yana kona zunubai da kuma wanke zukata daga kazanta. Haka nan, a wasu ruwayoyin, ana daukar Ramadan daya daga cikin sunayen Allah, wanda ke nuni da girma da daukakar wannan wata.
Daya daga cikin fitattun siffofin Ramadan shi ne wajibcin yin azumi a cikin wannan wata. Azumi yana nufin kamewa daga ci, sha, da sauran buda baki daga kiran sallar asuba har zuwa magariba. An jaddada wannan wajibcin na Ubangiji a cikin aya ta 183 a cikin suratu Baqarah, wadda ta nuna cewa azumi ba ibada ce ta zahiri kadai ba, a’a yana da aikin takawa, da kyautatawa, da kamun kai.
Watan Ramadan kuma watan ne na saukar wasu littafan sama. Bisa hadisai, an saukar da Littattafan Ibrahim, da Attaura, Linjila, da Zabura a cikin wannan watan. Wannan yana kara wa Ramadan muhimmanci da daukaka, inda ya zama wata na musamman na alaka da Allah da samun shiriyar Ubangiji, wanda a cikin Alkur'ani mai girma ya kira "Lailatul Kadri" yana daya daga cikin darare masu muhimmanci na shekara, kuma yana cikin watan Ramadan. Wannan dare yana da matsayi na musamman saboda saukar Alqur'ani da falalolinsa marasa adadi, kuma yin ibadarsa yana daidai da ibadar wata dubu.
A cikin watan ramadan, baya ga azumi, musulmi suna karatun kur’ani, da yin addu’o’i, da neman gafara, da kokarin neman yardar Allah ta hanyar kyautatawa da taimakon mabukata. Wannan wata wata dama ce ta komawa ga dabi'ar dan Adam mai tsafta da kusanci zuwa ga Allah. Don haka ne ma musulmin duniya ke maraba da wannan wata da nishadi da kuma cin gajiyar albarkar da ke cikinsa.