A rahoton shafin Al-Kafeel, Haramin Abbas (a.s) ya sanar da sunayen wadanda suka cancanci zuwa mataki na biyu na gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ta “Al-Ameed Prize” a bangaren manya.
Majalisar kula da harkokin kur’ani mai tsarki ta al-Abbas (a.s) ce ta dauki nauyin shirya gasar, kuma ta samu halartar mahardata daga kasashe 22, wadanda 30 daga cikinsu suna bangaren manya, 10 kuma a bangaren matasa.
Mutane 15 daga cikin 30 da suka shiga rukunin manya da suka hada da makaratun Iran uku ne suka tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar.
Sheikh Muhammad Bassiouni daga Masar, Bassem Al-Abidi daga Iraki, Mushtaq Al-Ali daga Iraki, Abdul Kabir Haidari daga Afghanistan, Muhammad Asfour daga Masar, Shaid Hassanein Al-Helou daga Iraki, Sayyed Karim Mousavi dan kasar Iran da kuma Muhammad Rimal dan kasar Labanon na daga cikin mambobin kwamitin alkalan gasar da suka jagoranci gasar.
Ya kamata a lura da cewa gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ta "Al-Ameed Prize" na daya daga cikin kokarin da mazhabar Abbasiyawa suke yi na yada al'adun kur'ani mai tsarki a matsayin wata hanya mai muhimmanci ta jin dadin daidaikun jama'a da al'umma, kuma masu karatu daga kasashen Larabawa da Asiya da Afirka sun halarci zagaye na biyu na wannan gasa da ake gudanarwa a cikin watan Ramadan.