IQNA – Mambobin tawagar matasa masu karatun kur’ani mai tsarki na kasar Iran sun gudanar da karatun ayoyi na 47 zuwa 49 daga cikin suratul Adh-Dhariyat a taro na biyu na sansanin horon da suka gudanar a farkon watan nan a birnin Qum.
Taron dai wani bangare ne na shirin shirya wannan tawaga a hukumance a watan Fabrairun shekarar 2025 da cibiyar kula da kur’ani ta Osveh, mai alaka da majalisar koli ta kur’ani.