IQNA

Alhazai Sun Ziyarci Makabartar Baqi Dake Madina

IQNA- Makabartar Baqi da ke birnin Madina mai alfarma a ko da yaushe ta kasance wuri mai tsarki da ruhi ga musulmi kuma ya zama wuri na musamman ga mahajjata daga kasashe daban-daban a yayin gudanar da aikin hajjin bana.

Wuri ne da zukatan muminai ke kafa alaka mai zurfi da tarihi da ruhi, kuma suke zaune cikin yanayi na natsuwa da addu'a. Bayan wannan ziyara ta ruhaniya da suka kai garin Baqi, mahajjata cikin saukin zuciya mai cike da bege, suka yi bankwana da Imaman (AS) da aka binne a can, sannan suka tafi Makka domin gudanar da aikin Hajji.