IQNA

Jagora Ya jaddada Bukatar Duniyar Musulmi ta Aiwatar da Darussan Aikin Hajji

14:19 - June 05, 2025
Lambar Labari: 3493367
IQNA - Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, akwai bukatar duniyar musulmi ta yi amfani da darussan aikin Hajji a yanzu fiye da kowane lokaci.

Jagoran ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya aikewa maniyyata aikin hajjin 2025 yayin da aka fara aikin Hajjin bana a Makka. Ga cikakken bayanin sakon:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga mafificin halittun Allah, Muhammad al-Mustafa, da alayensa tsarkaka, da sahabbansa zavavve da waxanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Hajji buri ne na mumini, Idin masu kwadayi, guzuri na ruhi na masu rabo. Idan ya kasance tare da sanin asalin ruhinsa, to ya zama magani ga manyan cutukan da ba al'ummar musulmi kadai ba, har ma da dukkanin bil'adama.

Aikin Hajji ba kamar sauran tafiye-tafiye ne da ake yi na kasuwanci ko yawon bude ido ko wasu dalilai ba, inda ayyukan ibada ko ayyukan alheri ke iya zama wani bangare na tafiyar.

Hajji shi ne shiri na yin hijira daga rayuwa ta yau da kullum zuwa ga kyakkyawar rayuwa, rayuwar tauhidi wacce a cikinta akwai tawafi (dawafi) a cikinsa a kewayen Axikin gaskiya [Ka’aba], ci gaba da sa’i [gudu tsakanin tsaunukan Safā da Marwah], dawwamammiyar ramiyya [jifa da duwatsu] na Shaidanun sharri, da wulakanci da shaiɗan. addu'o'i, ciyar da matalauta masu rauni da matafiyi da kallon kowane launi, jinsi, harsuna da mutane daga sassa daban-daban a matsayin daidai.

Kuma a kowane lokaci, mutum a shirye yake ya yi hidima, yana neman tsarin Allah, yana daga tutar kare gaskiya. Waɗannan su ne ainihin abubuwan da ke cikinsa, madawwama.

Aikin Hajji ya tattara a cikin kansa misalai na wannan rayuwa, ya san mahajjaci da waxannan misalan ya kuma kira su zuwa ga wadannan.

Ya kamata a kula da wannan gayyatar. Dole ne mutum ya buɗe zuciya da idanu don ganin duniya na waje da na ciki. Dole ne mutum ya koyi kuma ya tsaya tsayin daka kan kudurinsa na aiwatar da wadannan darussa a aikace.

Kowane mutum na iya ci gaba a kan wannan tafarki daidai gwargwado, amma malamai, haziƙai, waɗanda aka ba wa amanar siyasa da masu kishin al'umma ya kamata su yi fiye da sauran.

Duniyar Musulunci tana bukatar yin amfani da wadannan darussa a yanzu fiye da kowane lokaci. Yanzu dai karo na biyu kenan na aikin Hajji a daidai lokacin da bala'o'i ke faruwa a Gaza da yammacin Asiya. Kungiyar ‘yan ta’addan sahyoniyawan masu aikata laifukan da ke mamaye da Falasdinu tana da mugun zalunci da muguwar dabi’a da mugunta mara misaltuwa, sun dauki wannan bala’i a Gaza zuwa wani mataki na rashin imani.

Yara Falasdinawan yanzu ana kashe su ba kawai ta hanyar bama-bamai, harsasai, da makamai masu linzami ba, har ma da ƙishirwa da yunwa. Adadin iyalai da suke bakin ciki ga ‘yan uwansu, samarinsu, ubansu da uwayensu na karuwa kowace rana. Wanene ya kamata ya yi tsayayya da wannan bala'i na ɗan adam?

Babu shakka gwamnatocin Musulunci su ne suka fara gudanar da wannan aiki, kuma wajibi ne al'umma su nemi wannan mataki daga gwamnatocinsu. Kazalika gwamnatocin kasashen musulmi suna da sabanin ra'ayi na siyasa kan batutuwa daban-daban, amma hakan bai kamata ya hana su cimma matsaya da hadin kai kan mummunan halin da ake ciki a Gaza ba. Bai kamata ya hana su kare mutanen da aka fi zalunta a duniya a yau ba.

Wajibi ne gwamnatocin musulmi su toshe duk wata hanya ta taimako ga gwamnatin sahyoniyawan tare da kame hannayensu masu laifi daga ci gaba da wadannan munanan ayyuka a Gaza.

Amurka ce tabbatacciyar mai hannu a cikin laifukan gwamnatin Sahayoniya. Dole ne abokan Amurka a wannan yanki da sauran yankunan Musulunci su yi biyayya ga kiran kur'ani game da kare wadanda ake zalunta. Dole ne su tilasta wa gwamnatin Amurka ma'abota girman kan su kawo karshen wannan danyen aikin. Aikin bara’atu [bakin mushrikin] a lokacin aikin Hajji mataki ne a kan haka.

Tsayayyar abin al'ajabi da al'ummar Gaza suka yi, ya sanya batun Palastinu a kan gaba a cikin damuwar duniyar Musulunci da ma dukkan masu son 'yanci a duniya. Dole ne a yi amfani da wannan dama, kuma a yi kokari wajen ganin an gaggauta taimakon wannan al'umma da ake zalunta.

Duk da kokarin da ma'abota girman kan duniya da masu goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya suke yi na kawar da suna da duk wani abin tunawa da Palastinu, munanan dabi'un jagororin wannan gwamnati da manufofinsu na wauta sun haifar da wani yanayi da sunan Palastinu ke haskakawa a yau fiye da kowane lokaci kuma kiyayyar jama'a ga sahyoniyawa da magoya bayansu ya yi tsanani fiye da kowane lokaci. Wannan wata muhimmiyar dama ce ga duniyar Musulunci.

Masu magana da jama'a da masu zaman kansu dole ne su kara wayar da kan mutane da azancinsu tare da kara yawan bukatu game da batun Falasdinu.

Kuma ku alhazai masu albarka, kada ku yi sakaci da damar yin addu’a da neman taimakon Allah Madaukakin Sarki a lokacin aikin Hajji da rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi nasara a kan azzaluman sahyoniyawa da magoya bayansu.

Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tsarkakakken Zuriyarsa da Imam Mahdi (Annabi) Fiyayyen Allah da ya saura a bayan kasa- Allah Ya gaggauta bayyanarsa.

Gaisuwar Allah da RahamarSa da AlbarkarSa su tabbata a gare ku

Sayyid Ali Khamenei

Zul-Hijjah 3, 1446

30 ga Mayu, 2025

 

 

 

3493333

 

 

captcha