IQNA

Mutanen Yemen sun yi jerin gwanon taya murnar nasarar Iran a kan makiya yahudawan sahyoniya

19:53 - June 27, 2025
Lambar Labari: 3493458
IQNA - A yau 27 ga watan Yuni ne al'ummar kasar Yemen suka gudanar da gagarumin gangami a wasu lardunan kasar a wani bangare na ci gaba da gudanar da shirye-shiryensu na mako-mako na nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da tsayin daka da kuma taya Iran murnar nasarar da ta samu a yakin kwanaki 12 da ta yi da makiya yahudawan sahyoniya.

Rahoton Tashar  Al-Mayadeen ya ce al'ummar kasar Yemen sun gudanar da gagarumin gangami a lardunan Sa'ada, Rima, da Marib a wannan Juma'a, inda suke rera taken " taya murna ga nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma tare da Gaza ga nasara" a karkashin inuwar tsagaita bude wuta tsakanin Iran da gwamnatin sahyoniyawa.

An gudanar da wadannan taruka a manya da manyan dandali na garuruwa da yankuna daban-daban na lardunan Sa'ada, Rima, da Marib, kuma ana sa ran a yammacin yau dandalin "Al-Saba'in" da ke babban birnin Sanaa ma zai kasance wurin da miliyoyin jama'a za su halarta.

Har ila yau, an shirya gudanar da wani tattaki na nuna goyon baya ga Gaza da taya Iran murnar nasarar da ta samu a manyan mashahurai sama da 500 a birane da yankunan lardunan Al-Hodeidah, Hajjah, Abb, Amran, Taiz, Dhamar, Al-Jawf, Al-Mahwit, Al-Bayda, da yankunan lardunan Al-Dhale'.

 

 

 4291135

 

captcha