A cewar Al-Ilam Al-Harbi, kafar yada labaran yakin kasar Lebanon ta fitar da wani faifan bidiyo na Sheikh Naim Qassem, babban sakataren kungiyar Hizbullah, sanye da kakin yaki.
Bidiyon ya kunshi wasu sassa na jawabin Sheikh Naim Qassem na baya-bayan nan, inda ya nanata cewa Hizbullah ba za ta mika makamanta a kowane hali ba.
A cikin faifan bidiyon, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana kwance damarar gwagwarmayar da daukar rayukan al'ummar kasar Labanon.
Tun da farko, ofishin Netanyahu ya yi ikirarin cewa: "Yanzu ne lokacin da Isra'ila da Lebanon za su yi tafiya cikin ruhin hadin gwiwa, tare da mai da hankali kan manufa guda ta kwance damara na Hizbullah da samar da kwanciyar hankali da wadata ga bangarorin biyu."
Ofishin ya ci gaba da cewa: Idan sojojin kasar Lebanon suka dauki matakan da suka dace don aiwatar da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah, to Isra'ila za ta dauki matakan tunkarar matakin da suka hada da rage kasancewar sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sannu a hankali, tare da yin hadin gwiwa da tsarin tsaron da Amurka ke jagoranta.
A farkon watan nan ne majalisar ministocin kasar Lebanon ta amince da manufofin shirin da Amurka ke shirin yi na kwance damarar kungiyar Hizbullah.