IQNA

Jihad Islami:

Za a cimma kashi na biyu na yarjejeniyar tare da matsin lamba daga kasashen duniya kan Isra'ila

21:56 - January 03, 2026
Lambar Labari: 3494447
IQNA - A cikin wani jawabi da ya gabatar, Muhammad al-Hajj Musa kakakin kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu ya bayyana ma'auni na shawarwarin da kuma matakin da firaministan Isra'ila ke yi.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, ya bayyana a daren jiya Juma'a cewa, Benjamin Netanyahu ya yi fatan cewa tsarin mika gawarwakin fursunonin Isra'ila ba zai yi nasara ba, ta yadda zai yi wa kansa uzuri, tare da kawo karshen yarjejeniyar ta hanyar sake kai farmakin soja.

Al-Hajj Musa ya kuma yi tsokaci kan sakamakon ziyarar da firaministan Tel Aviv ya yi a birnin Washington na baya-bayan nan inda ya ce a yayin wannan ganawar, Donald Trump bai matsa wa Netanyahu lamba kan ya koma mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni ba, kuma bai tilasta masa amincewa da wannan mataki ba.

A karshe kakakin kungiyar Jihad Islami ya jaddada wajabcin sauya salon tafiyar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bayyana cewa, babban abin da zai kawo ci gaba a shawarwarin yana cikin matsin lamba ne kawai daga kasashen duniya.

Ya kuma jaddada cewa, babu wata hanyar da za a bi wajen komawa mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza ba tare da yin matsin lamba na hakika kan 'yan mamaya ba. A cewarsa, idan babu irin wannan matsin lamba, ba za a iya shawo kan matsalar da ake ciki a yanzu ba, da kuma cimma matakai na gaba na yarjejeniyar.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4326624

captcha