
Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya bayyana cewa, al’ummar kasar za su iya dakile duk wani shishigi da wuce gona da iri na Isra’ila a kan kasarsu ne idan suka hada kai.
Sheikh Na’im Qassem ya bayyana haka ne a yayin ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi wanda ke gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Lebanon.
Ya ci gaba da cewa, tun bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta fiye da shekara guda da ta gabata, har inda yau take Isra’ila ba ta mutunta wannan yarjejeniya ba, a maimakon haka ma a kullum rana tana kara hurumin kasar Lebanon ta hanyarb kai hare-hare a kan gidajen jama’a a kudanci da gabashin kasar, wanda ya zuwa yanzu hakan ya yi sanadiyyar kashe daruruwan fararen hula.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya nuna takaicinsa matuka a kan yanayin da ake ciki, musamman yadda Isra’ila take cin karenta babu babbaka a cikin kasar ta Lebanon, tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin dokokin kasa da kasa, tare da jaddada goyon bayan kasarsa 100% ga Lebanon wajen tunkarar wannan shishigi.
A yayin ziyarar tasa a kasar Lebanon, Araqchi ya gana da takwaransa na kasa da kuma shugaban kasa gami da Firayi minista da kuma shugaban Majalisar Dokoki, inda suka tattauna kan batutuwa da suka shafi alakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin.
4327851