
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Jumaa a yayin karbar bakuncin dubban mutanen da su ka kawo masa Ziyara daga birnin Qum, ya kuma ce; “Ya kamata kowa ya san cewa jamhuriyar musulunci ta Iran an kafa ta ne ta hanyar sadaukar da kan dubun dubatar mutane masu tsarkin niyya da daukaka, don haka ko kadan ba za ta yi sassauci wajen fuskantar masu barna ba.”
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya yi Ishara da kone-konen da wasu tsirarun mutane su ka yi a daren jiya da barnata gine-ginen kasarsu saboda kawai su farantawa shugaban kasar Amurka rai.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce, shugaban kasar Amurka wanda hannuwansa suke jike da jinin fiye da mutanen Iran 1000 da kuma kwamandoji da masana fasahar Nukiliya da su ka yi shahada a lokacin yakin kwanaki 12, ya yi furuci da cewa shi ne da kansa ya jagoranci yaki, amma yanzu ya fito yana cewa, yana goyon bayan al’ummar Iran,sannan kuma sai a sami wasu mutane da ba su san abinda yake faruwa su fito suna yin kone-kone.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ci gaba da cewa, to ya kamata kowa da kowa ya sani cewa ta hanyar sadaukarwar duban mutane aka kafa wannan jamhuriyar musuluncin don haka babu maganar yi wa masu barna sassauci. Haka nan kuma ya ce jamhuriyar musulunci ba za ta lamumnta da duk wani dankore ba.
Ayatullah Sayyid Ali Khamne ya kuma kara da cewa; Shugaban kasar Amurka yana Magana da duniya cikin girma da jiji da kai, to ya kamata ya sani cewa, masu dagawar duniya irin su Namarudu, Fir’auna, Riza Sha da dansa, Muhammad Riza Pahlawi duk sun ci kasa ne a lokacin da suke kan ganiyar ji da karfinsu.
Haka nan kuma jagoran juyin musulunci na Iran ya yi Ishara da maimaita kura-kurai da Amurka take yi akan alumar Iran da jamhuriyar musulunci ta Iran, sannan ya kara da cewa; Wadannan irin kurakuran suka kai Amurka ga cin kasa da faduwa a baya, a wanan lokacin ma babu makawa sai sun ci kasa.
Da ya tabo abinda yake faruwa a yankin Latin Amurka, jagoran juyin musulunci na Iran ya ce; suna killace wata kasa, sannan su fito a fili su bayyana cewa, sun yi hakan ne saboda man fetur, kamar yadda man fetur din Iran ya kasance a karkashin masu girman kai da kuma ‘yan sahayoniya da ‘yan korensu a baya.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Da izinin Allah jamhuriyar musulunci za ta ci gaba da bunkasa kowace rana,kuma makircin makiya zai ci kasa.
4327819