IQNA

A cikin sa'oi 24 da suka gabata Isra'ila ta kashe Falastinawa 15 a yankin zirin Gaza

19:23 - January 10, 2026
Lambar Labari: 3494478
IQNA- Majiyoyin Falastinawa sun bayar da bayanin cewa Isra'ila ta kashe Falastinawa 15 a cikin sa'oi 24 da suka gabata a yankin zirin Gaza.

Tashar Almasira ta nakalto daga majiyoyin Falastinawa cewa, a cikin sa'oi 24 da suka gabata Isra'ila ta kashe Falastinawa 15 a yankin zirin Gaza a ci gaba da karya yarjejeniyar dakatar dabude wuta datake yi.

Haka nan kuma rahotannin sun tabbatar dacewa,baya ga shahadar wadannan mutane wasu dadama kuma sun jikkata.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa, daga lokacin dakatar da bude wuta ya zuwa yanzu, Isr'ila ta karya wannan yarjejeniya sau dubu daya da 193.

Haka nan kuma rahoton ya kara dacewa,a cikin watanni uku da uka gabata bayan tsagaita wuta, motoci dubu 23 da 19 ne suka shiga yankin daukeda kayan agaji, alhali ya kamata motoci dubu 54 su shiga yankin dauke da kayan agaji a cikin wadannan watannin.

 

/4327867

captcha