
Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa,Majalisar koli ta addinin musulunci a kasar Malaysia ta goyi bayan jagoran juyin juya halin musulunci na Iran dangane da bayaninsa da ya dora wa Trump dukkanin laifin barnar da akayi a lokacin tarzoma a kasara cikin yan kwanakin nan.
Baya ga haka kuma
Fiye da fitattun malaman Musulunci 100 daga ko’ina cikin duniya sun bayyana goyon bayansu ga Iran da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na kasar a rikicin da ya girgiza kasar, wanda kasashen waje suka shirya.
Wadannan malamai, masana shari’a, da masana sun yaba wa jagorancin Ayatollah Seyyed Ali Khamenei da jajircewarsa a gaban makiya da shishigi na kasashen duniya.
A cikin wata sanarwa, sun bayyana duk wata barazanar kisan kai da aka yi masa a matsayin ayyana kiyayya ga dukkan al’ummar Musulunci.
Da suka ambaci ayoyi daga Alƙur’ani Mai Tsarki, sun bayyana ayyukan Shugaban Amurka Donald Trump da firainistan Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin “Muharrabeh” ma’ana masu (ƙiyayya ga Allah) da kuma “Cin hanci da rashawa a Duniya.
” Ayyuka kamar tsoratarwa ga jama’a, barazana ga tsaron ƙasa, da kisan gillar fararen hula.
Sun bayyana su a matsayin wadanda ke da alhakin rashin tsaro, tashin hankali, da kuma asarar da za a iya samu.
Wadanda suka sanya hannu kan wannan takarda sun zargi Isra’ila da Amurka kai tsaye da alhakin waɗannan ayyukan ta’addanci da ɓarna da suka haifar da mutuwar jami’an tsaro da fararen hula a Iran.
4329119