
Rahotanni daga kasar Australia na cewa, Cibiyoyin musulmi kimanin 50 a kasar sun nuna damuwa matuka dangane dasabbin dokokin da aka bullo da su a kasar domin takurawa musulmin kasar.
A taro wanda suka gudanar domin tattauna wannan batu,sun fitar da bayani na bai daya, wanda yake yin tir da Allawadai da sabbin dokokin da aka kirkira domin kawai a takura ma musulmi.
Bayanin ya kara dacewa, bisa la'akari dacewa musulmin kasar Australia 'yan kasa ne da suke da hakkoki kamar kowane dan kasa, babu wani dalili dazai sanya amayarda su saniyar ware a cikin kasarsu.
Baya ga haka kuma bai kamata a samarda dokoki wadanda suka yi karo da abin dayake a cikin kundin tsarin mulkin na baiwa dukkanin yan kasahakkokinsu na addini dakumakare wadannan hakkoki ba.
Australia ta kirkiri wasu sabbin dokoki na takura wa musulmi bisa hujjar hare-haren da aka kai kan yahudawa a lokacin da suke wani taro a kwanakin baya a kasar, inda suke dora alhakin hakana kan musulmi,ba tare da yin la'akari dacewa mutum da ya yi babbar sadaukarwa wajen dakile harin har da kashe maharin shi ma musulomi ne.
4329739/