
A cikin wani bayani da ta fitar Hukumar raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta yi Allawadai da kakkausar murya kan kisan daliban makaranta a wani hari da Amurka da Isra'ila suka kai kan makarantarsu a yankin kudancin kasar Iran.
Bayanin ya ce babu yadda kisan kananan yara daliban makaranta da ke daukar karatu a cikin ajujuwansu ya gamsar da duniya bisa kowace irin hujja ko dalili.
Wannan danyen aiki ne da ya sabawa dukkanin dokoki da ka'idoji na duniya, kuma dole ne a yi Allah wadai da hakan da kakkausar murya a inji hukumar.
A ranar Asabar din da ta gabata ce Jiragen yakin Amurka da na Isra'ila suka kaddamar da haria kan makarantar yara mata a yankin Minab da ke kudancin kasar Iran, inda suka kashe yara kusan 200 gami da jikkata wasu masu tarin yawa, ba tare da bayyana wani dalili ko hujjar yin hakan ba.
https://iqna.ir/fa/news/4337872