
Shaukat Mirzayiv Shugaban kasar Ozbakistan ya aike da sakon ta'aziyar Shahadar Jagoran Juyin juya halin muslunci. Ayatollah Sayyid Alli Khamenei ga shugaban kasar ta Iran Mas'ud Pezeshkiyan.
A cikin sakon ya bayyana cewa, yana mika ta'aziyyarsa da alhininsa ga dukkanin iyalan jagora da kuma sauran daukacin al'ummar kasar Iran.
Ya kara da cewa, tabbas rashin jagoran juyin juya halin muslunci babban rashi na al'umma baki daya, amma kuma duk da rashinsa da aka yi, ya bar ayyuka masu kima da daraja wadanda za su ci gaba da wanzuwa, kuma za a rika tuna shi da su a matsayin babbar gudunmawarsa ga al'umma.
4337902