IQNA

Nazarin Yaki Da Sahyuniyanci a cikin Alƙur'ani / 3

Rairaye muminai na gaskiya da kuma murkushe kafirai da munafukai a mahangar kur’ani

23:17 - March 07, 2026
Lambar Labari: 3494727
IQNA – A cikin wani bayaninsa jagora shahidin juyin juya halin musulunci ya bayyana matakai na tantance muminai da kuma rairaye su domin samun matsayi bayan cin jarabawa a mahangar kur’ani.

A cikin jawabin nasa jagoran ya bayyana cewa, akwai matakai wadanda suka zoa  cikin ayoyi daban-daban dangane da jarabawa ta ubangiji da kuma yadda yake aiwatar da komai nasa har zuwa ga sakamako na karshe.

1 – Mataki na farko bayan jarabawa shi ne domin Allah ya tantance muminai na gaskiya da kuma wadabda suke baragurbi masu raya imani da baki kawai.

2 – Mataki na biyu shi ne a lokacin da jarabawa ta zo ta fuskoki daban-daban musamman a wajen yaki ko kuma ta wasu hanyoyin da Allah yake jarabawa, yak an dauki shahidai daga cikin muminai da suka yi sadaukarwa a tafarkinsa.

3 – Mataki na uku daga nan sai Allah ya tsarkake muminai bayan sun ci jarabawa, ya tace zutansu daga duk wata gurbata, domin su zamanto masu tsarkin zuciya da kusanci da shi.

4 – Mataki na karshe shi ne kawo karshen kafirai da munafukai da suka cutar da muminai da kuma addinin Allah, wanda kuma shi ne mataki na karshe na samun nasara bayan kamala matakan jarabawa ga muminai.

Dukkanin wadannan abubuwa ne wadanda Allah madaukakin sarki yana yinsu domin rabautar bayinsa masu iklasi wadanda suke yin aiki domin neman yardarsa da kuma fatan samun sakamko daga gare shi.

 

 

captcha