
Da farko mutane suna zabar mambobin majalisar ne, su kuma sai zu zabi jagora tare da tantance shi.
Saboda haka a lokacin zabar jagora dole ne hakan ya zama a kan wasu ma’aunai na ilimi, da kuma masaniya kan gudanarwa.
Dangane da Ayatollah Mujtaba Khamenei akwai abubuwa masu muhimmanci da aka yi la’akari da su game da hakan. Na farko, ma’aunin iliminsa na zamani da na addini.
Ya yi karatu na tsawon shekaru a cibiyar Hauza ta Qom, ya yi karatu mai zurfi na fikihu da sauran bangarori a hannun manyan malamai da ake komawa zuwa gare su.
Na biyu, cikakkiyar masaniyarsa a kan tsarin kasar.
Tsawon shekaru yana da masaniya a kan yadda ake tafiyar da tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma daukar matakai masu sarkakiya na siyasa.
Na uku, alaka da kuma masaniya game da muhimman bangarori na kasar.
Masaniyar da yake da ita game da muhimman bangarori kamar Dakarun Kare Juyi da sauran bangarori, hakan ya ba shi damar sanin hakikanin lamurra ta fuskar tsaro da sauran fagage a Iran.
Na hudu, yanayin da ake ciki.
A yau Iran tana cikin wani yanayi da yake cike da kalubale,
Kama daga takunkumai da matsin lamba na tattalin arziki, zuwa matsaloli na yaki na kafofin sadarwa da kuma na tsaro.
A cikin irin wannan yanayin, da yawa suna da imanin cewa dole ne ya zama akwai Jagora, wanda yake da tunani da masaniya kan juyi, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na duniya.
Saboda haka ne masana da dama suke ganin cewa, zaben Ayatollah Mujtaba Khamenei da majalisar Kwararru suka yi, yana nufin ci gaba da bin tsarin siyasar Iran ne a ciki da waje, da kuma kiyaye tsarin ‘yancin kai na kasa da kuma fuskantar kalubale.
Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, duka wannan ya gudana ne bisa doka ta kundin tsarin mulki, da kuma zabe na mambobin da aka zaba da kuri’ar mutanen kasa.
Wannan shi ne abin da ya baiwa wannan zabe halasci na doka.