
Babban malami kuma Mufti na ahlussuna na kasar Pakistan Munib Rahman ya goyi bayan kasar Iran yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kantaa wannan wata na Ramadan.
Babban malamin ya bayyana wanann yaki da cewa yaki ne tsakanin gaskiya da karya, kuma Iran tana wakiltar dukkanin musulmi ne a wannan fafatawa da take makiya Allah.
Yaci gaba da cewa, bisa la'akari da irin matasayar da makiya musulunci suka dauka na shiga kafar wando daya da duk wata kasa wadda taki mika musu wuya, wanann ya sanya suna son ganin bayan Iran ko ta wace hanaya.
A kan haka ya ce wajibi ne a kan dukkanin musulmi su marawa kasar Iran baya a wannan yaki domin fuskantar makiya musulunci, domin idan ba musulmi basu hada kai yanzu ba, to kuwa tabbas za a murkushe kasashensu daya bayan daya.
4339941