
Haka A cikin wadannan ayoyi Allah ya bayar da tabbataccen lamuni ga muminai cewa tabbas idan kafirai suka yake su za su da baya, kuma ba za su samu wani maitaimako ba. ko jibintar lamarinsu ba saboda fito na fito da gaskiya da suka yi..
Abubuwa da dama suna faruwa wadanda suke a matsayin izina a gare mu, alhali hakan ya faru da na baya da suka gabata, duk da cewa Allah madauakin sarki ya kasan sanya abubuwan da suka faru da magabata su zama darasi ga 'yan baya da kuma abin koyi da kuma daukar darussa da suka dace.
Abin da ya faru a lokacin yakin Ahazab na jarabawa ga muminai yana daga cikin irin wadannan darussa da kuma abin buga misali na tsayin daka daga muminai masu imani da suke tare da manzon Allah, kuma an jaraba muminai aka girgiza su domin tantance masu imani na gaskiya da kuma masu raunin imani da ma munafukai daga cikin musulmi.