IQNA

Nazari Kan Yaki Da Sahyuniyanci A Cikin Kur'ani / 7

Tsayin Daka A yayin Fuskantar Makiya Da Kuma Ma'anar Nasara A kansu

22:23 - March 15, 2026
Lambar Labari: 3494745
IQNA- A yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan kasar Iran da kuma yadda kasar take fuskantar wannan babban yaki na makiyanta a kanta, za aiya daukar darussa daga ma'anonin ayoyin kur'ani mai tsarki.

Tabbas a bisa bayanin aya ta 22 a cikin Suratul Fathi da muka fara yana ishara da cewa, a wannan yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan kasar Iran da kuma yadda kasar take fuskantar wannan babban yaki na makiyanta a kanta, za aiya daukar darussa daga ma'anonin ayoyin kur'ani mai tsarki wanda suke tababtar da karfin imani na akidar musulunci a gaban makiya.


Abubuwa da dama suna faruwa wadanda suke a matsayin izina a gare mu, alhali hakan ya faru da na baya da suka gabata, duk da cewa Allah madauakin sarki ya kasan sanya abubuwan da suka faru da magabata su zama darasi ga 'yan baya da kuma abin koyi da kuma daukar darussa da suka dace.

Abin da ya faru a lokacin yakin Ahazab na jarabawa ga muminai yana daga cikin irin wadannan darussa da kuma abin buga misali na tsayin daka daga muminai masu imani da suke tare da manzon Allah, kuma an jaraba muminai aka girgiza su domin tantance masu imani na gaskiya da kuma masu raunin imani da ma munafukai daga cikin musulmi.

matsayar da muminai suka dauka wajen tunkarar kafircin duniya da ke neman ganin bayan duk wani mumini mai imani da tsayinm daka a gabansu, hakan yana a matsayin koyi da abin da muminai suka yi ne a ahzab da sauran wurare da aka kara tsakaninsu da makiya Allah a tarihin addinin musulunci tun lokacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

 

 

 

captcha