IQNA

Al-azhar: Rufe masallacin kudus da hana yin sallah a cikinsa laifi na kasa da kasa

23:05 - March 15, 2026
Lambar Labari: 3494746
IQNA - A cikin wani bayani da babbar cibiyar muslunci ta Azhar ta fitar ta bayyana cewa, Rufe masallacin kudus da hana yin sallah a cikinsa a matsayin laifi na kasa da kasa.

Jaridar Alharam ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da babbar cibiyar muslunci ta Azhar ta fitar ta bayyana cewa, Rufe masallacin da hana yin sallah a cikinsa laifi na kasa.

Bayanin na cibiyar AQzhar ya yi ishara ne da matakin da gwamnatin yahudawan sahyuniya suka dauka ne na rufe masallacin kudus a cikin wannan wata na Ramadan tare da hana dubban daruruwan musulmi yin salla a cikinsa.

Wannan shi ne karon farko da gwamnatin yahudawan sahyuniya ta dauki wannan mataki na hana yin duk wata salla a cikin masallacin Kudus, musamman a cikin watan da aka saba gudanar da salloli na tarawihi a kowace shekara.

Baya ga haka kuma ana gudanar da ibadar Itikafia  cikin masallacin kudus a kowace shekara da musulmi suke yi, amma a shekarar bana Isra'ila ta hana, domin kuwa ta kulle masallacin kuma ta killace shi da jami'an tsaro.

 

4340908

captcha