
Bayan yakin Uhud da kuma abubuwan da suka faru, da shidai da aka samu da kuma wadanda suka samu raunuka, ayata 137 a cikin suratu Ali Imran tana ishara da yadda aka bukaci muminai da su yi tadabburi da daukar darasi daga magabata, domin su ga yadda karshen wadanda suka karyata ayoyin Allah ya kasance.
Yakin Uhud yana daya daga cikin abubuwan buga misali a cikin tarihin musulunci, inda musulmi suka fuskanci jarabawa, amma kuma bisa hikima ta ubangiji da kyakkyawan jagoranci irin na manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka, musulmi sun yi amfani da hakan domin kara karfafa kansu da imaninsu.
Bayan nan Allah ya karfai muminai da cewa kada su samu rauni ko yin bakin ciki ko yanke kauna, matukar suna kan tafarkin gaskiya to kuwa tabbas su ne madaukaka indai har su muminai da gaske.
Sannan kuma Allah ya kara tausasa zukatansu da cewa, idan sun samu jarabawa a wanann yaki sun samu raunuka da kuma bayar da shahidai, to su ma kafirai sun samu irin wanann, sai dai bambancin shi ne su muminai a tafarkin gaskiya suke sabanin kafirai.
Allah ya kara da cewa wannan sunna ce daga cikin sunnoninsa, ya kan juya yanayi tsakanin mutane, wani lokaci a samu nasara wani lokaci kuma a samu jarabawa.