IQNA

An bude babban baje kolin madaba'antun Kur'ani mai tsarki na kasar Aljeriya

1:31 - March 17, 2026
Lambar Labari: 3494751
IQNA - Kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara a yau bunde babban baje kolin madaba'antun kur'ani mai tsarki na kasar Aljeriya.

Shafin yada labarai na Al-ittihad ya bayar da rahoton cewa, a yau bunde babban baje kolin madaba'antun kur'ani mai tsarki na kasar Aljeriya aka saba gudanarwa a kowace shekara.

A yayin wannan baje koli ana nuna kwafin kur'anai daban-daban da aka buga a madaba'antu na kasar Aljeriya, baya ga haka kuma akwai kur'anai da aka rubuta da hannu.

A kowace shekara a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma ana gudanar da irin wannan baje koli wanda yake samun hakartar madaba'antu daga ko'ina a cikin fadin kasar.


 

 

4341108

captcha