IQNA

Ali Larijani Babban Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasa A Iran Ya Yi Shahada

12:44 - March 18, 2026
Lambar Labari: 3494755
IQNA - Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Dr. Ali Larijani ya yi shahada, a wani da jiragen yakin Amurka da Isra’ila kai masa a Tehran.

Majalisar koli ta tsaron kasa a Iran ta bayar da sanarwar cewa, jiragen yakin Amurka da Isra’ila sun kai wa babban sakatarenta Ali Larijani hari a daren Talata a unguwar Pardis da ke cikin birnin Tehran.

Rahoton ya kara da cewa, Larijani ya yi shahada tare da dansa da kuma mataimakinsa, gami da wasu daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

Larijani ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru a kasar Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.

Daga cikin mukaman da ya rike hard a shugaban hukumar rediyo da talabijin na kasar Iran na tsawon shekaru masu yawa, haka nan kuma ya taba rike mukamin shugaban majalisar tsaron kasar a lokacin mulkin Ahmadinejad.

Sannan ya kuma zama mamba a majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci, kamar yadda ya zama shugaban majalisar dokokin kasar na tsawon shekaru 12 a jere.

Ya kuma zama babban mai baiwa jagoran juyin juya halin muslunci shawara kan harkokin siyasar kasa da kasa.

Bayan yakin da Isra’ila ta kaddamar a kan Iran a cikin watan Yunin 2026, Jagoran juyin juya hali ya sake nada shi a matsayin babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran, matsayin da ya yi shahada a kansa.

 

3496803

captcha