
Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar Noruz, Zahran Mamadani Magajin garin birnin New York na kasar Amurka ya jaddada matsayinsa na kin amincewa da yakin Amurka a kan Iran.
Magajin garin birnin New York musulmi na farko ya bayyana cewa, shi tun farko bai amince da wanann yakin ba, kuma yana yi wa Iraniyawa jajen abin da ya same su, da kuma fatan dukkanin alheri a gare su.
Ya jadda cewa, babu abin da yake yake jawowa ga bil adama illa asara da barna da rasa rayuka da dukiyoyi da haifar da rashin zaman lafiya, wanda kuma shi ne abin da shugaban Amurka yasanya a kasar a ciki.
4342008