IQNA

Nazari Kan Yaki Da Sahyuniyanci A Cikin Kur'ani / 13

Yahudawa da yadda suke haifar da Baraka a tsakanin musulmi

18:10 - March 23, 2026
Lambar Labari: 3494769
IQNA - A cikin watan radaman da ya gabata kowa yaga irin rawar da yahudawa suka taka a yakin da suke kaddamarwa kan Iran da kuma kokarinsu an haifar da Baraka tsakanin musulmi ta hanyar wannan yaki.

Daga cikin kabilun yahudawa a Madina akwai Aus da Khazraj, wadanda sun shahara a tarihin musulunci wajen kokarinsu na haifar da matsaloli ga musulmi, wanda ayoyin 98 zuwa 100 a surat Al Imran sun yi Magana a kansu.

Wadannan ayoyi masu albarka suna ishara da cewa, idan musulmi suka bi wani bangare na ahlul kitab, to zasu mayar da musulmi kafirai bayan imaninsu.

Larabawa bisa ga al’adarsu tun lokacin jahiliyya mutane masu saurin tasirantuwa da duk wani abu da ya shafi kabilanci, wanda hakan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya musulunci ya mayar da hankali matuka wajen tarbiyantar da musulmin farko kan fifita imani a kan kabilanci.

Wannan yana zuwa ne bisa ga yadda musulmin farko suka kasance sun fito daga larabawan jahiliyya wadanda suke dauke da irin wadanan halaye.

Ta hanyar yaudar wasu daga cikin musulmi a madina yahudawasun fara jansu a jiki, wanda hakan ya fara yin tasiri a kansu ba tare da sun lura ba, a kan haka Allah ya ja hankalinsu da cewa, su yi hattara da karkata ga yahudawa, domin zasu iya fitar dasu daga musulunci ba tare da sun Ankara.

A kan haka Allah yake kara jaddawa musulmi cewa yin riko da abin da manzon Allah yazo da shi na ayoyi daga Allah da ake karanta musu shi ne bababn gishiki da zai rike iamninsu.

 

 

3496827

captcha