
A cikin aya ta 190 a Suratu Baqarah, an yi siahara da abubuwa guda uku dangane da yaki da makiya, kan cewa yaki ya kasance saboda Allah ne wato a tafarkin ne ba a bisa wasu dalilai na daban ba. Sanann kuma yakin ya kasance wadanda suka yaki muminai, ba a yakar mutane kawai saboda su ba musulmi ba ne, sai wadanda suka yaki muminai suka cutar da su.
Bayan haka kuma ayar ta yi ishara da wani batu mai matukar muhimmanci shi ne yin adalci a cikin batun yaki, inda ayar ta ishara a fili kan cewa kada a wuce gona da iri, domin Allah madaukakin sarki baya son nasu wuce goda iri, ma'ana idan aka wuce gona da iri wajen mayar da martani a kan kafirai da suka yaki muminai, to za a shiga cikin wani abu wanda Allah baya so.
Dukkanin bangarorin ayar guda uku suna koyar da mu ladubba ne kan yadda ya kamata a tunkari makiya, kamar yadda aya ta 194 a cikin suratu baqara take kara tababtar da abin da ayar da ta gabata take yin ishsra a kansa, kan cewa idan wani yayi shishigi a kanku ku mayar da matani gwargwadon yadda ya yi shsishigi a kanku.
3496827