
Tashar Furat News ta bayar da rahoton cewa, Babban malamini addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani yana sanya ido kan yadda ake tatatra tatimako ga al'ummomin Iran da Lebanon wadanda suke fuskantar hare-haren ta'addanci daga Anurka da gwamnatin yahudawan sahyuniya.
Kafin wannan lokacin dukkanin wakilan Ayatollah sistania kasashe daban-daban sun sanar da umarninsa na wajabcin taimakon al'ummomin Iran da Lebanon, da kudade da duk abin da ya sawaka, domin samun sauki na wasu abubuwan da aka haramta musu saboda yaki.
Amurka da gwamnatin yahudawan sahyuniya sun fara kaddamar da hare-haren ta'addanci a kan Iran ne tun daga ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata, inda ya zuwa yanzu adadi mai yawa na fararen hula da jami'an tsaro suka yi shahada.