IQNA

Nazari Kan Yaki Da Sahyuniyanci A Cikin Kur'ani / 19

Fita Domin Tsayawa Tare Da Gaskiya Yana Nuni Da Hadewar Lamarin Musulmi A Mahangar Kur'ani

19:28 - April 04, 2026
Lambar Labari: 3494796
IQNA - Fita kan tituna domin tsayawa tare da gaskiya da kuma nuna baranta daga zaluncin masu girman kai manuniya ce ta haduwar kan al'umma bisa koyarwa ta kur'ani.

A cikin kur'ani mai tsarki a wurare daban-daban ana nusar da musulmi muhimmancin hada lamarinsu a wuri guda domin tunkarar makiya, domin kuwa sirrin nasarar musulmi ita ce hadin kansu a kan shugabancin da Allah ya umarce su da binsa.

A cikin aya ta 62 a cikin suratul Ahzab, an yi ishara da wasu daga cikin munafukai wadanda imani bai zauna a cikin zukatansu ba, yadda suka rika nuna halayya ta gazawa da tsoro da kin bin uamrnin manzon Allah a lokacin yakin handaq.

Ayar ta ishara karara da yadda wasu suka rika neamn uzuri domin su gudu daga wurin saboda abin da suka gani na hadari, duk da cewa wadanda suke da imani na gaskiya basu kallon hakan a matsayin hadari, domin kuwa sun Allah yana tare da su.

Baya ga haka kuma suna karkashin jagoranci da umarni na manzon Allah tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.
Ayar ta fallasa su da cewa suna neman uzuri ne da sunan sun bar gidajensu babu wata kariya, inda ayar tace karya suke yi suna dai son su gudu ne kawai.

A yau abin da muke gani a karkashin hare-haren zaluncin masu girman kai na duniya a kan kasar musulmi da kuma al'ummar musulmi an wannan kasa suke fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin tsayawa tare da gaskiya, hakan na nuni da gasgata alkawlin Allah ne da kuma yin tsayin daka a gaban masu jayayya da Allah.

 

3496958

captcha