
Mustafa Naqdi shugaban babbar cibiyar tarjama da ayyukan al'adua zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, daga cikin ayyukan da suka gudanar a baya-bayan nan har da arjamar kur'ani mai tsarki a cikin harsuna 14 fitattu na duniya a bisa mahanga ta mazhabar ahlul baiti.
Ya ce sun yi kokari matuka domin ganin cewa an gudanar da tarjamar bisa mahanga ta iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.
Sannan kuma ya yi ishara da cewa, domin gudanar da wanann aiki mai matukar muhimamnci, sun kokari sun samu mutane wadanda suke kwarewa matuka a cikin harshen larabci da kuma sauran harsunan da aka yi tarjama a cikinsu, domin komai ya kara fitowa fili ga mai karatu ya fahimci tarjamar ba tare da wata matsala ba.
Ya kara da cewa duk da cewa ba a ciki samun banbanci a wajen tarjama ba, an fi samun banbanci nea wajen tafsirin aya da kuma yadda ake gina shi bisa dalilai da mahanga, amma duk da haka sun yi kokari matuka domin ganin sun baiwa mahangar iyalan gidan manzon Allah hakkinta a cikin tarjamar.
Wannan cibiya tana gudanar da ayyuka daban-daban a bangaren tarjama ta littafan addini da kuma sauran ayyuka da suka shafi al'aladu na addinin muslunci.