
A yayin wata ganawarsa da manema labarai yau a birnin New York , Babban magatakrdan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci da a ci gaba da tattaunawar da aka fara tsakanin Amurka da Iran, tare da tabbatar da cewa ba a sake komawa yaki ba.
Ya ce wannan tattaunawear da aka fara bai kamata ta tsaya ba, ya zama wajibi ta ci gaba domin warware matsalolin ta hanyar lumana da diflomasiyya.
Guterres ya ci gaba da cewa, kowa ya ga illar da yakin ya yi wa duniya, baya ga barna da rasa rayuka wanda hakan ba abu ne mai kyau a rayuwa ba.
Sanann kuma ya yi ishara da tattaunawarsa da ministan harkokin wajen Pakistan, inda ya ce ya yi farin cikin jin cewa ana kokarin komawa tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, da zimmar ganin an kawo karshen yakin baki daya, wanda shi ne abin da kowa ke fata.
4346481