
A cikin wata makala da ta rubuta, Jaridar New York Times ta yi ishara game da batun lafiyar kwakwar shugaban kasar Amurka Donald Trump sakamakon abubuwan da yake wadanda sun yi hannun riga da dabiun mutum mai cikakken hankali da lafiyar kwakwalwa.
Jaridar ta ce tun kafin wannan lokacin akwai batutuwa da da dama da ake danganta su da matsalar kwakwalwa game da Donald Trump.
A cikin kwanakin nan ya yi wasu abubuwa da yawa wadanda suke sanya shakku game da hakan, inda hatta wadanda suke bashi uzuri a halin yanzu sun fara dawowa daga rakiyarsa.
Daga cikin maganganu da ya yi a baya-bayan nan har da cewa zai rusa Iran da tarihinta na dubban shekaru, wanda hakan ya yi hannun riga da kalamai na mutum mai cikakken hankali.
Baya ga haka kuma ya fito ya yi kalaman batunci ga jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika, bayan da ya mayar ma Trump da martani kan cin zarafin annabi Isa da ya yi.
4346473