
Jaridar Almadina ta bayar da rahoton cewa, A yau ne ake fara gasar hardar kur'ani mai tsarki ta farkoa yankin Kosovo da ke gabashin nahiyar turai tare da halartar matasa mahardata.
Wannan gasa dai ita ce irinta irinta ta farko da ake gudanarwa a wanann yankin wadda take samun halartar daruruwan matasa mahardata kur'ani mai tsarki.
Yankin Kosovo dai yana gabas masu kudancin nahiyar turai ne, inda kuma akasarin mazauna yankin mabiya addinin muslunci ne.
Yankin yana daya daga cikin yankunn da suka kasance karkashin ikon daular Usmaniya tun daruruwean shekaru dfa suka gabata, wanda haklan yasa musulunci ya yi tasiri a yankin.
Wannan gasar kur'ani wadda aka fara gudanarwa a yau zata ci gaba da waka har tsawon kwanaki masu zuywa a cikin wannan mako.
Daga karshe dai zaa fitar da sunayen wadanda suka kai ga mataki na kusa da na karshe da kuma na karshe, domin bayar da kyautuka ga wadanda suka lashe gasar.