IQNA

Jerin Gwanon Yin Tir Da harin Makarantar Minab A Birnin Hague

23:03 - April 17, 2026
Lambar Labari: 3494822
IQNA - Iraniya mazauna kasar Holand sun gudanar da jerin gwano domin nuna goyon bayansu ga iyalan yaran da Amurka ta kashe a makarantar Minab da ke Iran.

Iraniya mazauna kasar Holand sun gudanar da jerin gwano domin nuna goyon bayansu ga iyalan yaran da Amurka ta kashe a makarantar Minab da ke Iran.

An gudanar da wannan jerin gwano ne ba tare da rera wani take ba, dukkanin mutanen da ke cikin jerin gwanon sun yi tsit ne suna tafiya.

Wasu daga cikinsu suna dauke da tutocin Iran, wasu kuma suna dauke da hotunan jagoran juyin juya halin muslunci da ya yi shahada.

Wasu kuam suna dauke da hotunan yar 'yan makarantar Minab da Amurka ta kashe, a matsayin wata alama da ke nuna an tafka laifukan yaki ta hanyar aikata hakan.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a duniya da ma 'yan siyasa gami da cibiyoyin ilimi duk sun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da Amurka ta aikata, inda ta jefa bam a kan makarantar yara 'yan mata tare da kashe kimanin 168 daga cikinsu.

Baya ga haka kuma an kashe malamai da ma'akaita da dama a cikin makarantar, kamar yadda a daya bangaren 'yan mata na sakadandare ma an dalibai kimanin arba'in.

 

 

 

4346908

captcha