ayatullah sayyid ali khamenei - Shafi 3

IQNA

Jagora Ya Yi Kakkausar Kan Halin Da Musulmi Suke Ciki A Myanmar:
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka dangane da shiru da kuma halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa da masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suke yi dangane da kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar Myammar inda ya ce hanyar magance wannan matsalar ita ce kasashen musulmi su dau matakan da suka dace a aikace da kuma yin matsin lamba ta siyasa da tattalin arziki ga gwamnatin kasar Myammar.
Lambar Labari: 3481889    Ranar Watsawa : 2017/09/13

Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kuma ba za ta taba mika kai ga mulkin kama-karya na ma'abota girman kai, yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tsaya da kafafunta kyam sama da shekarun baya.
Lambar Labari: 3481762    Ranar Watsawa : 2017/08/03

Jagoran Juyin Islama:
Bangaren siyasa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana a lokacin wata ganawa da yayi yau din nan da shugaban Majalisar Koli ta kasar Iraki (ISCI) Sayyid Ammar Hakim da 'yan tawagarsa da suke ziyara a nan Tehran cewa, Amurka ba abin dogaro ba ce inda yayi watsi da ikirarin Amurka na cewa tana fada ne da kungiyoyin ta'addanci na kasar Iraki da suka hada da Da'esh da sauransu.
Lambar Labari: 3481024    Ranar Watsawa : 2016/12/11

Jagoran Juyin Juya Hali:
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a wata ganawa da yayi da dubun dubatan mutanen garin Esfahan, ya bayyana cewa a wurin Iran babu wani banbanci kan wanda ya lashe zabe a Amurka.
Lambar Labari: 3480959    Ranar Watsawa : 2016/11/21

Jagoran Juyin Islama:
Bangaren siyasa, a lokacin da yake zantawa da malamai da kuma limamai na birnin Tehran da kewaye, jagoran juyin juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana irin matsayin da masalalci yake da shi a acikin addinin musulunci da yada koyarwarsa acikin jama'a.
Lambar Labari: 3480736    Ranar Watsawa : 2016/08/23