IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Bai Kamata A Fada Cikin Yaudarar Amurka Da Murmuhsinta Ba

22:11 - December 11, 2016
Lambar Labari: 3481024
Bangaren siyasa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana a lokacin wata ganawa da yayi yau din nan da shugaban Majalisar Koli ta kasar Iraki (ISCI) Sayyid Ammar Hakim da 'yan tawagarsa da suke ziyara a nan Tehran cewa, Amurka ba abin dogaro ba ce inda yayi watsi da ikirarin Amurka na cewa tana fada ne da kungiyoyin ta'addanci na kasar Iraki da suka hada da Da'esh da sauransu.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Amurka ba da gaske take yi ba a ikirarin da take yi na kawo karshen ta'addancin kungiyoyi masu kafirta musulmi, face dai kokari ma take yi wajen kiyaye wasu kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin nan don cimma manufofinsu.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: A koda yaushe Amurka tana kokari ne wajen ganin kasashen musulmi ba su yi karfi da tsayuwa da kafafunsu ba, don haka sai yayi da cewa bai kamata a fada tarkon yaudarar Amurka ba.

Yayin da yake magana kan batun rashin ingancin dogaro da Amurka, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar a duk inda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi riko da wannan nasiha na rashin dogaro da Amurka to kuwa ta yi nasara, don haka sai ya kirayi al'ummar Iraki da su dogara da irin karfin da suke da shi, su nesance dogaro da Amurka.

Haka nan kuma ya yawaba mahukuntan kasar Iraki dangane da yadda suka yi kokari wajen ganin sun kunyata makiya, wadanda suke kokarin bayyana abin da yake faruwa akasar da cewa Magana ce ta banbancin mazhaba, inda ya ce Iraki tana yaki ne da ta’addanci, wanda ya samo asali daga kasashen da ke kirkiro ‘yan ta’adda domin bata sunan addinin muslunci.

Ya ce ko shakka babu ta’addanci bai san da zaman addini ba ko wata akida ta addini, akidar ta’addanci it ace kisa da shan jinni, kuma makiya muslunci sun yi hakan ne domin bata sunan addini inda suke amfani da wasu kasashe da ake kallonsu na muslunci waya yada akidar ta’addanci da sunan jihadi kamar yadda suke yi a Syria da Iraki, inda suke tura ‘yan ta’adda suna kasha msuulmi domin haifar da fitina da Baraka tsakanin musulmi.

Dangane da yadda aka kafa rundunar sa kai ta al’ummar Iraki kuma take a sahun gaba wajen yaki da ‘yan ta’adda, hakan ya kara tabbatarwa duniya cewa Iraki tana yaki da ta’addanci ne ba wata akida ta addini ba, domin kuwa wannan runduna da suke ta kokarin sun bayyanata a matsayin ta wani bangare, ta hada dukkanin bangarorin al’ummar Iraki ne har ma da wadeanda ba musulmi.

Shi ma anasa bangaren Hojjatol Islam Hakim ya yaba matuka da irin gagarumar gudunmawar da Iran take baiwa Irakia dukkanin bangarori, wanda babu abin da Irakawa za su ce kan hakan sai dai godiya, musamman irin rawar da Iran take takawa wajen hada kan al’ummar Iraki da kma gudunmawa ta soji a wajen yaki da ‘yan ta’adda afadin kasar.

3552868


captcha