IQNA

Mahanga Kan Nazariyar Yuga Ta Fuskacin Irfani Da Kadaita Mahalicci

Bangaren fikira, masu tunanin nazariyar nan ta Yuga da ake danganta ta da wani nauyin aiki da masu yin hakan suke raya cewa suna isa zuwa ga mahaliccin kowa da komai wannan nazariya tana tattare da kure.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Hoj. Eslam Dr. Muhammad Taqi Fali malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza, ya ce masu tunanin nazariyar nan ta Yuga da ake danganta ta da wani nauyin aiki da masu yin hakan suke raya cewa suna isa zuwa ga mahaliccin kowa da komai wannan nazariya tana tattare da kure bisa dalilai na hankali da kuma na nassi.
Wani mutum daga cikin muslmai da suke zaune a wajen birnin madina, hakika ya tambayi Manzom Allah da ya ayyana masa daren Lailatul kadr domin ya kebance kansa a cikinsa da ibada, sai Manzo ya ayyana masa daren ashirin da uku. to kila abin da yake nuni zuwa ga hakikanin wannan lamari shi ne cikakken bayani da ya zo a cikin ayyukan daren ashirin da uku.
Hakika wasu nassoshi sun yi magana game da haka kamar addu'a misali: "ya ubangiji nayi yammaci ina bawa gareka." Wanan shi ne abin da Imam Zainul Abidin yake yawaita addua'a da shi a cikin wannanan dare bisa abin da Kaf 'ami ya Rawaito, haka ma addu'ar Jaushunal Kabir da Sagir, domin wannan addu'ar tana kunshe da wasu abubuwa na musamman a layukan karshe guda uku, kari a kan abin dake tattare da ita na raya shi da ibada a cikin wannan dare.
Hakika daren goma sha tara ga wata an kebance shi da yawan yin Istigafari sau dari a cikinsa, da kuma tsine wa wanda ya kashe Amirul Mu’aminin Ali (as ) Sau dari, domin a wannan daren ne aka Sari Amirul Mu'aminina Ali (as) a cikinsa da hannun Abdurahman Ibn Muljam khariji (tsinuwar ubangiji ta tabbata gare shi)
Kamar yadda ake karfafa yin addu'oin nan guda biyu na musamman a cikin dararen watan ramadan kamar:" ya Ubangiji ka sanya a cikin al’amuran da ka hukumta kuma ka kaddara da kuma addu'ar ya wannan wanda ya kasance.
Amma daren ashirin da daya na daga cikin dararen da aka fi sani da dararen lailatul kadr shi ne wanda aka fi tsamamanin amun daren a cikinsa fiye da sauran wadanda suka gabata. daga nan sai ya fara ayyuka da addu'oin kwanaki goma na karshe na watan ramadan wanda aka kebance ta da su.
Yawaita rayasu da ibada, domin manzon Allah (saw) ya kasance yana nade shimfidarsa sannan ya zage damtsen sa wajen yin ibada a cikin kwanaki goma karshe na watan ramadan, ya kasance yana lizimtar masallaci ya dukufa a cikinsa.
Hakika an yi bayanai game da muhimmacin dake tattare da raya shi da yawan yin sallah da Addu'a da kuma salati ga manzo da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma tsine wa wadanda suka zalunci manzo da iyalan gidansa tsarkaka, tun da a cikinsa ne Amirul muminin Ali ya yi shahada (as) kuma ana so a yawaita karanta ziyarar Imam Hussain (as) a ranar.
Amma daren ashirin da uku shi ne mafificin dare kamar yadda muka ambata. Domin kuwa ya zo da wasu ayyuka na musamman a cikinsu, su ne karatun alkur'ani, musamamn ma wasu surori kebantattu, misali kamar Surar Ankabut, da Rum da Dukhan, da kuma surar Kadr sau dubu, haka ma ya karfafa game da karanta ziyarar Imam Hussaini (As).

Hakazalika karanta ziyarar Imamul Hujja (Af ) kamar haka: ya Ubanjigi ka sanya ga masoyinka alhujjatu binul Hassan salatinka su tababbata gare shi da iyayensa baki daya, a cikin wannan lokaci da ma kowanne lokaci masoya, da masu kiyayewa, da kuma jagoranci da mataimaki, da kuma hujjah har sai ka tababbatar da shi a cikin kasa, cikin nastuwa kuma ka rayar da shi a cikinta lokaci mai tsawo. An so a rinka maimaita wanann addu'ar a lokuta daban-daban kamar yadda yake mustahabi ne a hada ta da wasu Addu'oi da aka kawo a cikin littafan Addu'a.)
Daga karshe yana da kyau a yi la'akari da dararen lailatul kadr, domin ranar lailatul tana da matsayi na musamman da ya yi kama da darajar daren lailatul kadr, kamar yadda ya zo a cikin wasu ziyarori da aka yarda da su kuma ya yi kama da abin da daren lailatul kadr yake da shi da ranar juma'a.
Kamar yadda muka sani akwai wasu hukumce-hukumce da idodin nan guda biyu suka hadu a kai, ko kuma suka yi daidai ba tare da wani bambanci ba, misali: harmacin yin azumi a ranakun da kuma wajibcin yin sallar idi, ko kuma mustahabin yin su a cikin bayani da mallama fikihu suka ambata a cikin litattafansu, haka ma batun ciyarwa a ranakun ko kuma mustahabanci, da yin addu'a da ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki, hakika Ahlul Baiti sun jaddada game da wasu abubuwa masu yawa cikinsu.
929308