IQNA

Kisan Musulmin Afirka Ta Tsakiya Sakamako Ne Na Yin Shirun Al'ummomin Duniya

18:03 - February 24, 2014
Lambar Labari: 1379465
Bangaren kasa da kasa, an bayyana kisan gillar da ake yi wa musulmi a kasar Afirka ta tsakiya da cewa sakamako ne na nuna halin ko in kula da kasashen duniya suke yi kan batun, wanda hakan ya karfafa mabiya addinin kirista masu tsaurin ra'ayi wajen ci gaba da aikata wannan mummunan aiki. Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa

, a zantawar da ta hada shi dad an majalisar dokokin kasar Chadi Muhammad Ibn Zain ya bayyana cewa, kisan gillar da ake yi wa musulmi a kasar Afirka ta tsakiya da cewa sakamako ne na nuna halin ko in kula da kasashen duniya suke yi kan batun mai hadari matuka.

A wani rahoton kuma Faransa ta ce an sami raguwar tashe-tashen hankula a cikin kasar Afrika ta tsakiya, babban kwamandan sojan Faransa da ke kasar Afirka ta tsakiya Franscisco Soriano ya fada a jiya lahadi cewa; Bayan da sojojin Faransa su ka shiga cikin kasar ta Afrika ta tsakiya an sami koma bayan rikici da fadace-fadacen bangaranci da ke faruwa a cikin wannan kasa.

Janar Soriano ya ci gaba da cewa; A karkashin shirin kwance damarar yaki ta kungiyoyin da su ke fada a kasar, kawo ya zuwa yanzu an kwace makaman zamani da na gargajiya da su ka kai dubu biyar da kuma hada manyan makamai.

Jami’in sojan na Faransan ya yi wannan maganar ne a daidai lokacin da kae ci gaba da kashe musulmi a cikin kasar ta Afirka ta tsakiya da kum tilasta wasu daga cikinsu yin hijira zuwa waje, a wani labarin daga kasar ta Afrika ta tsakiya, dakarun tarayyar Afirka na zaman lafiya sun yi kokarin hana guduwar kwamandojojin kungiyar kiristoci masu fada da musulmi ta “Anti Baleka” daga gidan kurkuku.

A wani bayani da dakarun tabbatar da zaman lafiya na tarayyar Afirka suka fitar, sun ambaci cewa; Wasu kwamandojin kungiyar ta Anti Baleka biyu tare da hadin bakin  shugaban kurkuku, sun yi kokarin guduwa, sai dai an dakile kokarin nasu.

1378500

Abubuwan Da Ya Shafa: afirka
captcha